Matakai Zuwa Wurin Kristi

1/14

MATAKAI ZUWA WURIN KRISTI

GABATARWA

Kalmomin nan, “Ku z0 gareni” suna faduwa kan kunnuwa masu- yawa-wannan kira na Maceci mai-tausayi wanda zuciyarsa ta kamna tana matsa kurkusa da dukan wadanda suna barin Allah; kuma cikin zukatan mutane da dama, wadanda suna kokarin neman taimako daga cikin Yesu, nufin komawa ga gidan Uban yana hanzarta. Tambayar da Toma ya yi “Yaya za mu san hanya?” yakan zo wa irin wadannan. Yakan zama kamar gidan Uban yana da nesa, kuma hanyar takan zama da wuya da shakka. Wadanne matakai ne suna bishewa zuwa gida? MK iii.1

Kan wannan Littafi yana fadan aikin ta. Yana nuna Yesu wanda shine kadai yana iya biyan bukatun rai, yana kuma bi da kafafuwan masu shakka da masu tsayawa zuwa “tafarkin salama.” Yanabi da mai-nema zuwa adalci da ruskawan hali, mataki da mataki, kan hanyar ran Kristi, zuwa ruskawan nan na albarka da ake samu cikin cikakken bayaswar kai da bege mara-jijjigawa cikin alheri na ceto da kuma ikon kiyayewa na Abokin masu-zunubai. Koyaswa da ana samu cikin wadan nan shafofi ta kawo ta’aziyya da bege zuwa wurin rayuka da yawa masu damuwa, ya kuma sa masu-bin Ubangiji da yawa su yi tafiya tare da bege da kuma murna cikin matakan Shugaba mai-tsarki. An kafa bege cewa zata iya kawo sako cfayan ga wadansu kuma wadanda suna bukatan taimako dayan. MK iii.2

‘‘Bari hanya ta bayyana a wurin Matakai har zuwa sama.” Haka ne ya faru wa Yakub lokacin da aka tsananta masa da tsoron cewa zunubin sa ya raba shi da Allah, ya kwanta domin ya huta, sai “ya yi mafalki, ga tsani a kafe a kasa, kansa ya kai har sama.” Haduwar sama da kasa ya bayyana gareshi, kuma kalmomin ta’aziyya da bege suka zo wa cfan yawon nan daga wurin wanda ya tsaya kan matakan inuwa. Bari a maimaita wannan wahayin sama ga mutane da yawa yayinda suna karanta wannan labari na hanyar rai.Masu - bugawa. MK iii.3